Tinubu Ya Yi Allah-Wadai Da Kashe-kashen Jos Da Kaduna
• Dole A Kamo Wadanda Suka Kashe Mutane a Angwan Rukuba — Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fito ya yi Allah-wadai da kakkausar murya game da hare-haren rashin imani da wasu ‘yan bindiga suka kai a gundumar Angwan Rukuba da ke Jos, Jihar Filato, da kuma kauyen Kahir da ke Karamar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna.
Shugaban ya bayyana wadannan hare-hare, wadanda suka hada da kisan jama’a a Jos da kuma garkuwa da baki ’yan bikin aure a Kaduna, a matsayin babban kalubale ga hadin kan Najeriya. Ya kuma tabbatar wa ‘yan kasa cewa ba za a zura ido wadanda suka aikata wannan danyen aikin su sha da dadi ba.
A cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa kan fannin Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata, Shugaba Tinubu ya bayyana maharan a matsayin azzalamai kuma matsorata.
> "Duk wanda zai fake da duhun dare ya kashe mutanen da ba su da kariya kamar yadda aka yi a Jos da kauyen Kahir, to matsoraci ne marar tausayi. Manufar wadannan maharan ita ce su haifar da ramuwar gayya domin jini ya ci gaba da kwarara," in ji Shugaban.
Shugaba Tinubu ya ba wa jami’an tsaro umarnin su kara kaimi wajen kamo wadanda suka aikata laifin da kuma wadanda ke yada labaran karya da nufin ruruta wutar rikici. Haka kuma, ya ja kunnen wasu bangarorin kafafen yada labarai da ke kokarin danganta hare-haren da batun addini.
Babban matakin da Shugaban ya dauka sun hada da:
* Kiran Jami'an Tsaro: Ya bukaci jami'an tsaro su rika amfani da bayanan sirri don dakile hare-hare kafin su auku.
* Ceton Wadanda Aka Sace: Ya ba da umarnin gaggauta ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su a kauyen Kahir.
* Kayayyakin Aiki: Ya bayyana cewa gwamnati na kan hanyar sayo manyan makaman zamani don bin sawun miyagun mutane a duk inda suke.
Shugaban ya jinjina wa Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato da Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna bisa kokarinsu na shawo kan lamarin da kuma tallafawa ayyukan ceto.
0 Comments