Ni a suwa: Ba zan taba kuskura na raina shugaba Buhari ba, inji Bola Tinubu
legit.ng
Jun 3, 2022 9:28 PM
Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas da ke neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya ce ba zai yiwu ba ya raina shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya, TheCable ta ruwaito.
Tinubu ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, dangane da kalaman sa da ya yi a taron da ya yi da deliget-deliget na jam’iyyar APC a jihar Ogun.
A ganawar da ya yi da su a ranar Alhamis, Tinubu ya ce in ba dan shi ba, da Buhari ya fadi zaben shugaban kasa a 2015.
Sai dai a cikin sanarwar da ke fayyace kalaman nasa, Tinubu ya ce ba wai yana nufin muzanta shugaban kasa Buhari bane.
'Karin Bayani: Ba Zan Taɓa Raina Buhari Ba, In Ji Bola TinubuA cewarsa:
0 Comments