Nigeria Custom Service, NCS Recruitment 2025, Shortlisted Candidates, Kwastam Nigeria, Sunayen wadanda aka dauka
Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta bayyana sunayen waɗanda suka samu nasarar shiga jerin waɗanda aka tantance domin sabon zagayen daukar ma’aikata.
Bisa bayanan da aka fitar:
Arewa ta samu mutane 541,
Kudu kuma mutane 1,244.
Wannan na nufin cewa gaba ɗaya, mutane 1,785 ne aka ɗauka daga sassan ƙasar nan gaba ɗaya.
Hukumar ta ce za a ci gaba da tantancewa domin tabbatar da cewa duk wanda aka zaɓa ya cika ƙa’idojin cancanta, kuma za a sanar da wuraren ganawa da jadawalin gwaje-gwaje nan gaba kaɗan.
Ana shawartar waɗanda suka nemi aikin su duba shafin yanar gizon hukumar don tabbatar da sunansu da samun ƙarin bayani kan matakin gaba.
0 Comments