Vijay Thalapathy ya dakatar da gangamin siyasa saboda suka daga ‘yan adawa
Jarumin fina-finan Indiya, Vijay Thalapathy, ya dakatar da gangamin siyasar da yake yi, bayan cece-kuce da suka biyo bayan matakinsa na shiga harkokin siyasa.
Rahotanni na cewa jam’iyyun adawa a jihar Tamil Nadu na ta suka da caccakar jarumin, suna zarginsa da yin siyasar “siyan alfarma” kamar yadda ake zargin wasu ‘yan takara a kasar.
Vijay, wanda shi kansa ne ya kafa sabuwar jam’iyya, ya ce dakatarwar da ya yi ta gangamin siyasa ta na da nufin bai wa jam’iyyarsa damar sake nazari kan dabarun ta kafin ci gaba da yakin neman zabe.
Masu lura da lamuran siyasa a Tamil Nadu na cewa, zuwan jarumin cikin siyasa ya tayar da kura da dadewa aka daina gani, inda wasu ke ganin yana da tasiri matuƙa musamman ga matasa.
0 Comments