Yanzu-Yanzu: FIFA Ta Cire Maki Daga South Africa Saboda Ɗan Wasa Mara Izini

Yanzu-Yanzu: FIFA Ta Cire Maki Daga South Africa Saboda Ɗan Wasa Mara Izini

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA ta sanar da cewa an cire wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Afirka ta Kudu (Bafana Bafana) maki a wasan cancantar gasar cin kofin duniya.
Dalilin wannan hukunci shi ne saboda ƙungiyar ta saka Teboho Mokoena, wanda bai cancanta ba, a cikin wasa da suka yi da Lesotho.

FIFA ta bayyana cewa sakamakon wasan da aka tashi 1–0 yanzu an juya shi zuwa 3–0 a nasarar Lesotho. Hakan ya sanya South Africa ta rasa maki uku a cikin rukuni na cancantar gasar duniya.

Wannan hukunci na iya shafar tsayar da ƙungiyar a teburin cancantar gasar, tare da rage musu damar zuwa World Cup 2026.

A yanzu haka, ƙungiyar Lesotho ta ƙaru da maki kuma ta samu damar hawa sama a jadawalin rukuni.

Post a Comment

0 Comments