1. Very Dark Man Ya Tona Asirin Dillalan Wayoyi Daga China

Allah ya sakawa wannan mutumin da alkhairi!

Ɗan gwagwarmaya Very Dark Man ya tona asirin dilolin Najeriya da ke siyo wayoyi daga ƙasar China 🇨🇳.

“Very Dark Man” ya ziyarci ƙasar China tare da yin bidiyo yadda dillalan wayoyi ke cutar al’umma a Najeriya.

Ga wasu daga cikin tone-tonensa:

1️⃣ Mafiyawan sababbin iPhones da ake siyarwa a Najeriya tsofaffi ne aka gyara aka saka cikin kwalin sabo.

2️⃣ Idan batirin iPhone ya lalace, ana yin boosting ɗinsa zuwa 100% domin ruɗar mai siya.

3️⃣ Wayoyin da ake kira “UK Used” duk ƙarya ce, daga China ake zowa da su. Kasar UK ba ta fitar da wayoyin da aka yi amfani da su.

4️⃣ Screen, Battery, Charger, USB, da sauran kayan haɗi duk fake ne daga China, amma ana siyar da su da sunan original.

5️⃣ Dillalan Najeriya suna ninka farashin wayoyi da yawa:
- iPhone 11 Pro Max – ₦200,000 a China, ₦450,000 a Najeriya.
- iPhone XR – ₦120,000 a China, ₦300,000 a Najeriya.

A takaice: Wannan binciken ya nuna cewa al’umma na bukatar **ilimi kafin siyan waya**, musamman daga masu siyar da “UK Used” ko “sabbi”.


Tambaya: Ka taɓa sayen waya da ta lalace da wuri? Ka bar mana ra’ayinka a ƙasa 👇

Post a Comment

0 Comments