China ta nuna sabbin jiragen yaƙinta na J-35 a bainar jama’a karo na farko

China ta nuna sabbin jiragen yaƙinta na J-35 a bainar jama’a karo na farko
China a ranar Lahadi ta bayyana hmsabbin  jiragen yaƙinta na J-35 da J-35A masu ɓoyayyen fasaha (stealth), a karo na farko ga jama’a, kamar yadda jaridar Global Times ta ruwaito, ta ambaci wata kafar labarai da ke da alaƙa da rundunar sojin kasar.
Bidiyon da China Military Bugle ta fitar ya nuna jiragen J-35 da J-35A waɗanda ba su da fenti suna cikin aikin haɗawa a kamfanin Shenyang Aircraft Company Limited, wani reshe ne na Aviation Industry Corporation of China (AVIC) mallakar gwamnatin kasar. 
J-35, wanda aka sani da jirgin yaƙin farko mai ɓoyayyen fasaha da aka ƙera a cikin gida, ya kammala horon farko na tashi da sauka wajen amfani da na’urar jefa jiragen sama ta lantarki (electromagnetic catapult) a kan jirgin ruwan yaƙin kasar mai suna Fujian.
Haka kuma, J-35A — wanda ke ɗauke da nau’in jirgin da ake amfani da shi daga ƙasa — ya kasance cikin hotunan da aka nuna.

An ƙera J-35A ne don ya zama muhimmin ɓangare na dabarun yaƙin sama na “stealth” da “counter-stealth”, kuma babban aikinsa shi ne tabbatar da mallakar sararin samaniyar kasar, duk da cewa yana da ƙwarewar kai hare-hare  ƙasa da sama.
Rahoton ya bayyana cewa muhimman manufofin jirgin sun haɗa da:

sarrafa sararin samaniya,

yaƙi da jiragen abokan gaba,

kai hari kan cibiyoyin kariyar sama da na ruwa,

tare da lalata jiragen yaƙi ko wani iri ne, masu ɗaukar bama-bamai, yana dauke da makamai masu linzami a jikinsa

Post a Comment

0 Comments