Koriya ta Arewa ta yi gargadin hukunta duk wata kasa da ta raina ta

Koriya ta Arewa ta yi gargadin hukunta duk wata kasa da ta raina ta


Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ya ce ƙasarsa ta shirya hukunta kowace ƙasa da ta nuna mata raini ko barazana.
Kim ya bayyana haka ne yayin da yake duba sabon jirgin yaƙin ruwa mai suna Choe Hyon, wanda aka gina don, a cewarsa, “hukunta masu tayar da hankali daga ƙasashen maƙiya.”
Jaridar gwamnati ta ƙasar, KCNA, ta ruwaito cewa Choe Hyon na ɗaya daga cikin manyan jiragen yaƙin ruwa guda biyu da aka ƙaddamar a bana — wani ɓangare na shirin Kim na ƙarfafa ƙarfin sojojin ruwa.
A cewar Kim, wannan jirgin mai nauyin tan 5,000 “shaida ce ta yadda Koriya ta Arewa ke ci gaba da ƙarfafa tsaronta da fasahar yaƙinta, musamman a bangaren ruwa.”
Ya jaddada cewa sojojin ruwa na ƙasarsa za su yi amfani da wannan ƙarfi don kare ikon ƙasa, da kuma hukunta maƙiya da ke neman tayar da hankali.

Post a Comment

0 Comments