DA DUMI-DUMI: Mun bada cikakken hadin kai ga hukumar EFCC domin a bincike mu nida sauran ma'aikatan hukumar NAHCON, domin tabbatar da gaskiya, tare da jaddada cewa ba za ta kare duk wanda aka samu da laifi ba, inji shugaban hukumar NAHCON Farfesa Sheikh Abdullahi Sale Pakistan.

A yanzu haka EFCC ta kama wasu manyan jami’an hukumar biyu, su ne Aliu Abdulrazak, kwamishinan kula da ma’aikata da kudi, da Aminu Y. Muhammed, darektan kudi, domin cigaba da bincike. 

Rahotanni daga jaridar The Guardian sun bayyana cewa Farfesa Usman ya amsa gayyatar EFCC a babban ofishinta da ke Abuja, inda aka tambaye shi kan yadda aka gudanar da wasu kudaɗe da suka kai kimanin ₦50 biliyan da suka shafi shirye-shiryen aikin Hajji na 2025.

Bayan tambayoyi, hukumar ta bashi umurnin komawa gida, amma ta umarce shi da ya rika bayyana kansa a ofishinta kullum yayin da bincike ke cigaba akan hukumar ta su. 

Abubuwan da ake bincike a kai sun hada da; 

Amfani da ₦25 biliyan wajen biyan kuɗin tantuna a Masha’ir ba tare da cikakken izini ba.

₦7.9 biliyan da aka ce an ware don masaukin gaggawa.

₦1.6 biliyan da aka yi amfani da shi wajen tafiyar matan wasu jami’an gwamnati. 

Muna Addu'ar Allah ya bayyana gaskiya.

Post a Comment

0 Comments