YANZU-YANZU: Lauyoyi A Abuja Suɲ Shigar Da Ƙorafi Gaban Babban Lauyan Amurka Kan Soworē, Sun Nēmi A Binciki Harkokinsa Na Kuɗi, Haraji, Dakatar Da Bizarshi, Da Sauransu

YANZU-YANZU: Lauyoyi  A Abuja Suɲ Shigar Da Ƙorafi Gaban Babban Lauyan Amurka Kan Soworē, Sun Nēmi A Binciki Harkokinsa Na Kuɗi, Haraji, Dakatar Da Bizarshi, Da Sauransu
Wani rukuni na lauyoyi da ke Abuja sun shigar da ƙorafi gaban Babban Lauyan Jihar Nēw Yørķ, dake  Amurķã, suna nemaɲ a binciki harkokin kuɗi na Sahara Media Group Incorporatēd da mai mallakarta, Mista Omoyele Sowore.
Lauyoyin, a cikin ƙorafi da aka shigar a madadinsu ta hannan gungun wasu lauyoyi  Heartland Advisors & Solicitors, wanda aka rubuta a ranar 7 ga Oktoba, 2025, kuma aka mika shi a ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja jiya, sun kuma nemi “a dakatar ko a soke takardun tafiyar Sowore na Amurķa.”
Abubuwan da aka nema a cikin ƙorafin da Barrister Sunday Oluwole da Barrister Felix Olanrewaju Wolemiwa suka sanya wa hannu sun haɗa da;
“Binciken takardun kuɗi na Sahara Media Group Inc., ciki har da tallafin MacArthur Foundation, don tabbatar da bin dokokin ƙungiyoyin da ba sa yin riba na jihar New York,  a bincika ko kuɗin da Sahara Media Group Inc. ta tara ana amfani da su ne bisa manufar taimako ko kuma ana karkatar da su zuwa ayyukan na ƙashin kai ko siyasa, da kuma duba takardun haraji na mutum da kamfanin Mista Sowore don tabbatar da bin dokokin haraji na Amurka, musamman dangane da kuɗaɗen da ke tallafawa gidansa da rayuwarsa a Amurka.”
Ƙorafin mai taken “Request for Investigation into Financial Activities of Sahara Media Group Inc. and Mr. Omoyele Sowore,” ya ce;
“Mun rubuto ne cikin girmamawa don neman ofishinku ya duba harkokin kuɗi na Sahara Media Group Inc., wani kamfani da aka yi rajista a New York, da wanda ya kafa kamfanin, Mista Omoyele Sowore, ɗan Najeriya da ke zaune a Amurka. Wannan buƙata ta samo asali ne daga damuwa kan yiwuwar rashin daidaito a cikin rahotannin kuɗin ƙungiya mara riba, biyan haraji, da bayyana kadarori, wanda ka iya yin tasiri ga jama’ar Amurka da Najeriya.

“Mista Sowore, wani shahararren ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Najeriya (2019, 2023), yana gudanar da Sahara Media Group Inc., wacce ke gudanar da Sahara Reporters. Takardun jama’a suna haifar da tambayoyi game da gaskiyar bayanan kuɗin ƙungiyar da kuma bayanan kuɗi wanda mutun ke biya  na Mista Sowore, musamman la’akari da ayyukan siyasa da yake gudanarwa a ƙasashen waje.”

Sun bayyana manyan abubuwan da ke damunsu da suka haɗa da; kuɗin ƙungiya mara riba da bayyana gaskiya, inda suka nuna cewa Sahara Media Group Inc. ta karɓi tallafin dala miliyan 1.3 daga MacArthur Foundation (2016–2019) don horar da ’yan jarida a Najeriya, kuma suka zargi cewa rahotannin jama’a kan yadda aka yi amfani da waɗannan kuɗaɗe sun yi iyaka sosai, wanda ya haifar da damuwa kan bin dokokin ƙungiyoyin da ba sa yin riba na jihar New York da ke buƙatar gaskiya da amfani da kuɗaɗen taimako ta hanya mai dacewa.

Game da rashin daidaiton bayyana kadarori, lauyoyin sun zargi cewa
“A shekarar 2023, Mista Sowore ya bayyanawa Hukumar Zaɓen Najeriya (INEC) cewa yana da gida guda a Najeriya mai darajar ₦5 miliyan da kuma mota irin ta 2008 Toyota Camry. Sai dai takardun jama’a sun nuna cewa ya sayi wani gida a Amurka kimanin shekarar 2018, mai darajar kusan dala $552,000, wanda ba a bayyana shi ba a cikin takardun INEC. Wannan yana haifar da tambayoyi kan yiwuwar ɓoye kadarori ko yin rantsuwa da karya ƙarƙashin dokar Najeriya, tare da yiwuwar matsalar haraji a Amurka idan ba a bayar da rahoto ba.”

Suna ɗagi ayar tambayoyi kan ƙarfin kuɗin Sowore da yadda yake gudanar da  rayuwarsa, inda lauyoyin suka ce:
“Rahotanni suna nuna cewa ɗan Mista Sowore yana halartar makarantar Dwight-Englewood School da ke New Jersey, inda kuɗin makaranta na shekara ya kai kusan $59,235 (2024–2025). Wannan, tare da kuɗaɗen da aka kashe a harkokin siyasa a Najeriya, ba ya dacewa da ƙarfin kuɗin da Sahara Media Group Inc. ke da shi, wacce ke aiki a matsayin kafar yada labarai. Binciken tushen kudin sa da bin haraji zai iya fayyace ko wadannan kudaden suna fitowa daga halattattun hanyoyi ne.”

Sun kuma ce:
“A shekarar 2018, wata gungiyar bada taimako mai suna GoFundMe ta dakatar da wani taron tara kuɗi na dala miliyan 2 da aka kafa domin tafiyar ‘Take Back Nigeria Movement’ ta Mista Sowore saboda damuwa kan manufarta. Duk da cewa daga baya aka dawo da asusun, wannan lamari yana bukatar kulawa don tabbatar da cewa kuɗin da aka tara a New York sun yi daidai da dokokin tara kuɗin taimako.”

“Dangane da ikon ofishinku na kula da ƙungiyoyin da ba sa yin riba da aka yi wa rajista a New York, ina roƙon da a duba takardun kuɗi na Sahara Media Group Inc., ciki har da tallafin MacArthur Foundation, don tabbatar da bin dokokin ƙungiyoyin da ba sa yin riba na New York (misali, N-PCL § 112), a bincika ko kuɗin da Sahara Media Group Inc. ta tara ana amfani da su ne bisa manufar taimako ko kuma ana karkatar da su zuwa ayyukan kai ko siyasa, a duba takardun haraji na mutum da kamfanin Mista Sowore don tabbatar da bin dokokin haraji na Amurka, musamman dangane da kudaden da ke tallafawa gidansa da rayuwarsa a Amurka, sannan a dakatar ko a soke takardun tafiyarsa na Amurka.

“Wannan buƙata an yi ta ne cikin gaskiya domin ƙarfafa ɗabi’ar warware gaskiya, tare da kare amincin ƙungiyoyin da ba sa yin riba a New York da kuma amincewar jama’a kan harkokin siyasa tsakanin ƙasashe.”

Post a Comment

0 Comments