YANZU-YANZU: Jirgin agaji ɗaya ya tsira, wanda ke kan hanyarsa na zuwa Gaza.

YANZU-YANZU: Jirgin agaji ɗaya ya tsira, wanda ke kan hanyarsa na zuwa Gaza.

Isra’ila ta tare kusan dukkanin jiragen ruwan Flotilla, sai wani jirgi mai suna. Marinette, shine kadai ya tsira daga Garkuwar Isra'ila.

Marinette shi ne kaɗai daga cikin jiragen Global Sumud Flotilla da ya ci gaba da tafiya zuwa Gaza bayan ya tsallake toshewar da rundunar sojin ruwan mamayar Isra’ila ta kafa.

Anadolu Ajansi ta ruwaito cewa, masu shirya tafiyar jiragen sun bayyana a shafin Instagram cewa, jirage 41 ne aka tare da karfi ba bisa ka’ida ba a wani farmaki da Isra’ila ta kai cikin awanni 12.

“An Isra'ila tayi garkuwa da Fararen hula ba bisa ka'ida ba,” in ji sanarwar. “Duniya ta shaida abin da ke faruwa idan fararen hula suka kalubalanci kulle. Duk da haka – Marinette na ci gaba da tafiya.”
Kungiyar International Committee to Break the Siege on Gaza (ICBSG) ta ce Marinette na cigaba da tafiya, sai dai tana da nisa sosai saboda jinkirin da aka samu sakamakon matsalolin inji.

Sumud Flotilla ta tabbatar da cewa fiye da ’yan gwagwarmaya 450 daga ƙasashe 47 aka kai su tashar jiragen ruwa ta Ashdod a kudancin Isra’ila. Wadanda aka kama sun hada da ’yan ƙasashen Spain, Italiya, Brazil, Turkiyya, Girka, Amurka, Jamus, Sweden, Birtaniya, Malaysia, Faransa da wasu da dama.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Isra’ila ta ce a cikin sanarwa cewa, za a tantance waɗannan masu fafutukar a Ashdod kafin a mayar da su Turai.
Anadolu, ta ambaci gidan talabijin na jama’a KAN a Isra’ila, ya ruwaito cewa rundunar ruwan kasar ta kama jirage 41 da ke dauke da kusan mutum 400 a yayin da suke kan hanyarsu zuwa Gaza. KAN ya kara da cewa dukkanin jiragen za a ja su zuwa tashar Ashdod.
A cewar masu shirya, dakarun ruwan Isra’ila sun kewaye jiragen, sun katse siginal da sadarwa kafin su ja su zuwa tashar. Wasu daga cikin masu fafutukar sun wallafa bidiyo a yanar gizo da ke nuna jiragen rundunar ruwan Isra’ila na kusantowa suna ba da umarnin sauya hanya.

Jiragen ruwan, dauke da kayan agaji da magunguna, sun tashi daga ƙarshen watan Agusta. Wannan ne karo na farko cikin shekaru da kusan jiragen 50 suka tashi tare zuwa Gaza dauke da daruruwan masu goyon bayan farar hula.

Isra’ila ta ci gaba da kulle Gaza – inda mutane kusan miliyan 2.4 ke zaune – tsawon kusan shekaru 18. An kara tsaurara kullen a watan Maris lokacin da aka rufe hanyoyin shiga da fita tare da hana abinci da magunguna, lamarin da ya jefa yankin cikin yunwa.

Tun daga watan Oktoba 2023, hare-haren bam na Isra’ila sun kashe fiye da Palasɗinu 66,200, mafi yawansu mata da yara ne. Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun sha gargadi cewa Gaza na dab da zama wurin da ba za a iya zama ba, kuma zata iya zama trihi, inda yunwa da cututtuka ke kara yaduwa cikin sauri.Kamar Yadda Dan jaridar – Bernama-Anadolu ya bayyana.

Post a Comment

0 Comments