🛑 YANZU-YANZU: Najeriya ta fara shirin rage farashin man fetur


🛑 YANZU-YANZU: Najeriya ta fara shirin rage farashin man fetur

Gwamnatin Najeriya ta ce tana cikin tattaunawa da manyan kamfanonin mai domin rage farashin fetur a kasar.

Ministan makamashi ya ce gwamnati ta fahimci wahalar da jama’a ke ciki saboda tsadar rayuwa, musamman tsadar sufuri da abinci. Ya kara da cewa cikin ‘yan makonni masu zuwa, ana sa ran za a kawo sauƙi.
Masu sharhi sun ce wannan mataki zai zama wata sabuwar hanya ta saukaka rayuwar al’umma, idan aka kammala shirin yadda ya dace.

Yanzu idan aka samu nasarar rage farashin, zai taimaka matuka wajen rage tashin farashin kayayyaki a kasuwanni.

Post a Comment

0 Comments